Yadda aka sace matan Dapchi a watan jiya

Yadda aka sace matan Dapchi a watan jiya

'Yan gungiyar ta’addan Boko Haram sun kai hari a kauyen Dapchi da ke Arewa maso Gashin Nijeriya in da suka yi nasarar satar ‘yan Mata 110 na makarantar garin. Linius Unah yay i tattaki zuwa garin domin jin gaskiyar abunda ya wakana lokacin da kuma zantawa da iyayen yaran da aka sace.

Yadda aka sace matan Dapchi a watan jiya
Yadda aka sace matan Dapchi a watan jiya

A ranar 19, ga watan Fabrairu da misalign karfe 6:30 na yamma, Fatima Auwal ta je kicin din makaranta domin karbar abincin dare a makarantar Mata ta Kimiyya da Fasaha, a garin Dapchi.karbar abincin nata ke da wuya ta fara jin karar harbin Bindiga kafin ta ankara abun har yazo cikin makarantar tasu.

‘Yan Ta’addan sun shigo suna sanye da kayan Sojoji da kuma Motoci masu budadden baya, daga farko muna ta murna mun dauka sojoji ne suka zo dan su taimaka mana sai da naga wasu da Silipas a kafar su wasu kuma ko takalman ma babu sannan na gane ba sojojin kwarai bane.

DUBA WANNAN: INEC ta tasa qeyar ma'aikacinta har gaban hukuma

Adam Muhammed Kontoma ya na Sallah ne a masallacin bakin hanya lokacin da aka kai harin, ya ce ya na tina lokacin da suka zo suna ta ce ma mutane ba sunzo dan su cuci kowa bane suna neman makarantar mata ne, inda wani ya kaisu makarantar primary wanda sukayi barazanar kashe shi idan bai kaisu makarantar da suke nema ba, anda sun gane a karshe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng