Ga wani abu akan matar Sarki: Hanyoyi 5 da za’a iya bi don kubuta daga kamuwa daga cutar zazzabin Lassa

Ga wani abu akan matar Sarki: Hanyoyi 5 da za’a iya bi don kubuta daga kamuwa daga cutar zazzabin Lassa

Wani mummunan annoba da a yanzu haka yake yaduwa a Najeriya shi ne zazzabin ciwon Lassa, wanda ake samunsa daga cin duk wani nau’in abinci da beraye suka sanya baki akansa.

Gidan talabijin na The Channels ta ruwaito akalla mutane 110 ne suka mutu a sanadiyyar cutar a cikin shekarar 2018, don haka ya zama wajibi mutane su tashi haikan don shawo kan wannan annoba.

KU KARANTA: Bamu da wani takamaimen aiki banda zaman fada – Inji Sarakuna ga Buhari

Alamomin cutar sun hada da zazzabi ko masassara, yawan gajiya, ciwon kai, zafi a makogoro, ciwon kirji, tari, kumburar fuska, fitar jinni daga baki ko al’aura, daga nan kuma lamari ya ta’azzara.

Ga wani abu akan matar Sarki: Hanyoyi 5 da za’a iya bi don kubuta daga kamuwa daga zazzabin cutar Lassa
Zazzabin cutar Lassa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito manyan hanyoyin da cutar ke yaduwa sun hada da taba fitsari, miyau ko jinin bera, da kuma kulawa da mai dauke da cutar, amma a yanzu haka an gano hanyoyin da za’a iya bi don kauce ma cutar, hanyoyin kuwa su ne:

- Tabbatar da tsaftan gida a koyaushe

- A ajiye kayan abinci, musamman hatsi a cikin kwanukan da bera ba zai iya fasawa ba

- A nesanta bola daga gida

-Yin feshi akai akai na ragewa taruwan bera a gida

- Ajiye Kyanwa a gida ma na taimakawa wajen fatattakar beraye daga gida

A wani labarin kuma, cutar zazzabin Lassa ta kashe kanana yara 20 a garuruwan jihar Jigawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng