Hukumar Kwastan tayi wani wawan kamu yau a Legas
A ranar Litnin 5, ga watan Maris, 2018 da misalign karfe 4, kungiyar jam’an tsaro masu kula da gidajen Ajiyar kaya wadda Kwantrola Mutallib Sule, sukayi bincike a wani gida dake No. 6 Opebi Road, Ikeja a jihar Lagos, in da suka fidda kaya da suka kai darajar N1,732,857,393.96.
Shugaban kula da ayyuka na Kwastam, Muhammed Uba, ya ce sun kama wani dan kasar sin da kaya na kimanin naira biliyan daya
Mr Li Chaomin, dan kasar Sin ne aka kama tare da wadannan kaya, wanda ya say a zama dan kasar na biyu da aka kama da laifin shigowa da kaya wanda kasar Najeria ba ta yadda da a shigo da su ba.
A ranar Litnin 5, ga watan Maris, 2018 da misalign karfe 4, kungiyar jam’an tsaro masu kula da gidajen Ajiyar kaya wadda Kwantrola Mutallib Sule, sukayi bincike a wani gida dake No. 6 Opebi Road, Ikeja a jihar Lagos, in da suka fidda kaya da suka kai darajar N1,732,857,393.96.
Kungiyar kasuwanci ta Duniya (CITES 1973), ta nuna Hukumar ta Kwastam ke da hakkin kula da daddobin daji a kowace kasa a duniya ta hanyar hana kusuwanci na fitar dasu zuwa wata kasa ba kan ka’ida ba. Wanda ana kokarin a kawar da dabbobin da ake tatsar mai gdaga jikin su da ga doron kasa.
Don gudun shakku, hukun cin da muka dauka ya na cikin dokar aikin Kwastam sashe na 147 (CEMA) Cap 45, na dokar Najeriya ta 2004. Kayayyakin da aka karba da wadan da aka kama tare da kayan za’a mika su zuwa Hukuma don Karin bincike da sanin yanda za’a kula da dabbobin kasa.
DUBA WANNAN: Ko ka kafa hukumar Peace Corp ko kuma mu muyi - Sanatoci
Zanyi amfani da wannan dama wurin mika godia ga ma’aikatan mu bisa ga jajircewa a kan gudanar da aiki tukuru wurin ganin sun hana shiga da hita a kasar nan, za kuma mu cigaba da kara masu karfin gwiwa don su yi aiki yanda ya kamata.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng