An hallaka mutane 24 sakamakon wata sabuwar rikici da ta ɓarke a jihar Benuwe
Akalla gawarwaki 24 ne aka gano biyo bayan wata sabuwar rikici da ta barke a kauyen Omusu, wanda ta kunshi yan kabilar Idoma, dake cikin karamar hukumar Okpokwu na jihar Benuwe.
Kaakakin Kwamishinan Yansandan jihar Joel Yamu ya tabbatar da mutuwar mutane 16 da fari, mata 14 kananan yara 2, sai dai jaridar Daily Trust ta ruwaito an sake gano wasu sabbin gawarwaki guda takwas, hakan ya haura adadin matattun zuwa 24.
KU KARANTA: Kaico! Cutar sanƙarau ta yi ajalin ƙananan yara guda 9 a jihar jigawa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu yan garin suna fadin daga cikin matattun akwai wani Magidandi da matarsa mai dauke da juna biyu, sai kuma wani karamin yaronsu guda daya, haka zalka an raunata wani yaro mai shekaru 7 tare da kashe uwarsa.
A yayin ziyarar da Gwamnan jihar Samuel Ortom ya kai kauyen, ya yi kira da kama dukkanin masu hannu cikin lamarin, haka zalika ya umarci a shirya gawarwakinsu don binnesu a sati mai zuwa, bugu da kari ya yi kira da a kama shuwagabannin kungiyar Miyetti Allah, wanda ya zarga da kai hare haren.
Daga karshe gwamnan ya umarci hukumar bada agajin gaggawa na jihar, SEMA da ta kai ma all’ummar kauyen dauki, sa’anann ya shawarci mutanen da kada su dauki doka a hannunsu, kuma ya basu tabbacin za’a jibge jami’an tsaro don basu kariya.
Shima nasa jawabin, shugaban karamar hukumar yace ya samu korafi daga wasu yan Fulani kan cewa an sace musu dabbobinsu a kauyen, inda ya kira taron gaggawa don yin sulhu, amma suna cikin taron ne ya kara samun wani rahoton cewar Fulani sun kaddamar da hare hare a kauyen.
Shima shugaban Fulani a karamar hukumar Otupko, Ardo Risku ya shaida ma majiyar mu cewar baya gari yayi tafiya, amma ya samu labarin lamarin, kuma ya yi alkawarin bin diddigi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng