Rikicin jihar Taraba: Bamu da wani takamaimen aiki banda zaman fada – Inji Sarakuna ga Buhari
Sarakunan gargajiya na jihar Taraba sun koka kan irin tsarin mulkin Najeriya da ya mayar da su ba a bakin komai ba, ta hanyar hana su wani muhimmin iko, duk da cewa su ne makusanta al’umma.
Shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar Taraba, Aku-Uka Wukari, Sehakarau Agyo ne ya bayyana haka a yayin ganawarsu da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ziyarar kwana daya da ya kai a ranar Litinin.
KU KARANTA: Kaico! Cutar sanƙarau ta yi ajalin ƙananan yara guda 9 a jihar jigawa
Taron wanda ya gudana a fadar gwamnatin jihar ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga bangaren makiyaya, manomo,a hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shuwagabannij majalisa da kuma manyan jami’an gwamnatin jihar dake Jalingo.
Daily Trust ta ruwaito an shirya taron ne domin kowanne bangare ya bada labarin halin da suke ciki game da rikicin kabilanci da kuma na makiyaya da manoma da ya adda al’ummar jihar, sa’annan shugaba Buhari ya ji da kunnensa.
Sarkin yace sarakunan gargajiya iyayen al’umma ne, amma fa baya da zaman fada da shiga motocin alfarma, amma basu da wani takamaimen aiki, musamman duba da irin tashe tashen hankula da ake samu.
“Mune masu adanan al’adun gargajiya, amma ba mukamanmu a suna ne kawai, don haka babu abinda zamu iya tabukawa a sha’anin mulki, amma da ba haka ba, ai da tuni mun shawo kan rikice rikicen da muke gani a kullum.” Inji shi.
Da yake mayar da martani, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba da bayanin Sarkin, sa’annan yace tun dai Sarakuna na karkashin Sarki ne, ya kamata gwamnan jihar ya duba yiwuwar raba musu takaimaimen aikace aikace don magance afkuwar rikicin da jihar ke fama da shi a gaba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng