Yan sanda sun damke tantirin dan daba da makamai, bama-bamai da kayan sojoji
Wani kasurgumin dan daba kuma wanda ya shahara da fasa bututun mai, Temona Alison, wanda aka dade ana nema ruwa a jallo ya shiga hannu a jihar Bayelsa
Jami’an yan sanda sun damke Alison ne a ranan Lahadi, a gidansa dake Tombia-Ammassoma.
Wata majiyar hukumar yan sanda ta bayyanawa jaridar Southern City News cewa an damke shi tare kananan bama-bamai 4, kayan sojoji, adda da sauran su.
Kakakin hukumar yan sanda na jihar Bayelsa, Mr. Asinim Butswat, ya tabbatar da wannan rahoto.
Zaku tuna cewa a kwanakin bayan hukumar soji sun hallaka shahrarren dan daba, Don wani, tare da wasu yaransa a jihar Enugu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng