Noman shinkafa : Audu Ogbe yayi karya – Jakadan kasar Thailand

Noman shinkafa : Audu Ogbe yayi karya – Jakadan kasar Thailand

- Audu Ogeb ya ce gwamnatin Thailand ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da zama sanadin karyewar manyan kamfanonin sarrafa shinkafar kasar Thailand

- Jakadan Thailand zuwa Najeriya ya ce rahoton da Ogbe ya fitar akan karywar kamfanonin sarrafa shinkafar Thailand karya ce

Wattana Kunwongse, Jakadan kasar Thailand zuwa Najeriya, yace rahoton da Ministan harkan noma da raya karkara na Najeriya, Audu Ogbeh, ya fitar na cewa kasar Thailand ta na zargin Najeriya da zama sanadin karyewar manyan kamfanonin sarrafa shinkafar Thailand guda bakwai saboda Najeriya ta daina shigo da shinkafar karya ce.

A wata wasika da jakadan ya aikawa kamfanin Jaridar PREMIUM TIMES a ranar Talata, Jakadan ya zargi ministan da juya ainihin maganar da suka yi da juna.

Ministan harkan noma da raya karakara, Audu Ogbeh, yace gwamnatin Thailand ta zargi gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da zama ummulaba’sin karyewar manyan kamfanonin sarrafa shinkafar ta guda bakwai, saboda dakatar da shigo da shinkafar Thailand zuwa Najeriya da Buhari yayi.

Noman shinkafa : Audu Ogbe yayi karya – Jakadan kasar Thailand
Noman shinkafa : Audu Ogbe yayi karya – Jakadan kasar Thailand

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin taron da fadar shugaban kasa ta gudanar da manyan dilolin takin zamani da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jagorantar da kan sa a ranar Juma’a, 2 ga watan Fabrairu, a Abuja.

KU KARANTA : Rikicin Taraba ya fi na Benuwe da Zamfara muni – Buhari

Ogbe yace jakadan Thailand ya fada mi shi haka a lokacin da ya ziyarci shi a watan Fabrairu.

A jawabin da ministan yayi, yace jakadan kasar Thailand, ya fada masa cewa, karyewar manyan kamfanonin sarrafa shinkafa kasar Thailanda yasa rashin aiki yin a kasar ya karu daga kashi 1.2% zuwa kashi 4%.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel