Majalisar wakilla ta yanke shawarar binciken kwamacalar zaben yara a jihar Kano

Majalisar wakilla ta yanke shawarar binciken kwamacalar zaben yara a jihar Kano

'Yan majalisar wakillan Najeriya sun bayyana matsayar su biyo bayan kwamacalar zaben kananan yara da ake zargin an tafka a zaben kananan hukumomin da ya gabata a jihar a kwanakin baya inda suka bayyana cewa za su binciki lamarin.

Daga nan ne ma kuma dai sai majalisar suka dora alhakin binciken ga kwamitin majalisar dake kula da harkokin zabe da jam'iyyu domin farawa sannan kuma ya kawo wasu rahoto cikin sati 5.

Majalisar wakilla ta yanke shawarar binciken kwamacalar zaben yara a jihar Kano
Majalisar wakilla ta yanke shawarar binciken kwamacalar zaben yara a jihar Kano

KU KARANTA: Badakalar fansho: Majalisar wakillai ta kirawo ministar Jonathan

Wasu daga cikin 'yan majalisaun da suka tofa albarkacin bakin su game da lamarin, sun bayyana takaicin su ga yadda zaben ya gudana sannan kuma suka bukaci da ayi sahihin bincike domin hana sake faruwar hakan nan gaba.

A wani labarin kuma, Wani kwamitin dake binciken kwa-kwaf a kan harkokin kasa na majalisar wakillai ya aikewa da uwar gida Okojo-Iweala dake zaman tsohuwar shugabar kwamitin gyara da garambawul na harkokin 'yan fanshon kasa da sammaci bisa zargin almundahana.

Majiyar mu ta Premium Times haka zalika ta ruwaito cewa majalisar ta wakilai ta aika mata da sammacin ne don ta zo tayi masu karin haske game da sauye-sauyen da ta jagoranci kawowa a harkar ta fansho tun daga shekarar 2010.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng