Ziyarar Buhari: Gwamnatin jihar Filato ta sanar da ranar hutu ga ma'aikata

Ziyarar Buhari: Gwamnatin jihar Filato ta sanar da ranar hutu ga ma'aikata

Gwamnatin jihar Filato dake a yankin Arewa ta tsakiya ta sanar da bayar da hutu ga dukkan ma'aikatan ta a jihar domin samun damar tarbar shugaba Muhammadu Buhari da zai ziyarci jihar a ranar Alhamis 8 ga watan Maris.

Shugaban ma'aikatan jihar Mistam Izam Azi shine ya sanar da wannan matakin da gwamnatin ta dauka a jiya Talata jim kadan bayan gama wani taron tattaunawa na gaggawa da majalisar zartarwas kasar ta gudanar.

Ziyarar Buhari: Gwamnatin jihar Filato ta sanar da ranar hutu ga ma'aikata
Ziyarar Buhari: Gwamnatin jihar Filato ta sanar da ranar hutu ga ma'aikata

KU KARANTA: Magu ya taso tsohuwar ministar Jonathan a gaba

Legit.ng ta samu cewa kuma haka zalika kwamishinan yada labarai na jihar Mista Yakubu Dati ya bayyana cewa a yayin ziyarar ta shugaban kasa, za'a takaita tafiye-tafiye na jama'a musamman ma a kokuwar birnin Jos.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a jiya Talata ya bayyana cewa kungiyar ta'addancin Boko Haram kawo yanzu ba ta da wani katabus din da za'a rika maganar ta a kasar duk kuwa da sabbin hare-haren da ta kai a makarantar kwana ta 'yan mata a Dapchi da kuma kauyen Rann a jihar Borno a yan kwanakin nan.

Sai dai da ya ke karin haske, shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan hare-haren na ta'addancin babu gwamnatin da ke iya hana yin su dun kuwa da irin tsaron da ke gare ta a kasa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel