Rayuwar bariki: An garkame budurwar da ta yanki 'yar uwar ta a fuska da reza

Rayuwar bariki: An garkame budurwar da ta yanki 'yar uwar ta a fuska da reza

- Wata budurwa, Loveth Augustine, ta gurfana gaban kotu bayan tayi yunkurin yiwa wata makahon ido a gidan rawa

- Ana tuhumar ta da laifin yunkurin yin lahani a gaban kotu majistare ta Ikeja dake Legas

- Dan sanda mai gabatar da kara, Inspekta Raji Akeem, ya ce laifin budurwar ya saba da sashe da 170 da na 173 na kundin aikata laifuka na jihar Legas 2015

Wata budurwa Loveth Augustine mai shekaru 20 tayi yunkurin yiwa wata mata makahon ido bayan ta yanke ta da reza a fuska.

An gurfanar da budurwar a gaban kotun majistare dake Ikeja a jihar Legas bisa tuhumar ta da yunkurin yin lahani ga bil'adama.

Rayuwar bariki: An garkame budurwar da ta yanki 'yar uwar ta a fuska da reza

Rayuwar bariki: An garkame budurwar da ta yanki 'yar uwar ta a fuska da reza

Dan sanda mai gabatar da kara, Inspekta Raji Akeem, ya shaidawa kotu cewar Loveth ta aikata laifin ne a ranar 20 ga watan Fabrairu da ya wuce.

KU KARANTA: Yadda gawa ta farfado bayan likitoci sun tabbatar da ya mutu

Ya kara da cewar fada ne ya kaure tsakanin Loveth da wata mata, Motunrayo Fatai, a wani gidan rawa da misalin karfe 1:00 na dare.

Loveth ta lakadawa Motunrayo duka tare da yi mata rauni da reza a yunkurin ta na kokarin yi mata makahon ido.

Laifin Loveth ya saba da sashe na 170 da na 173 na kundin hukuncin aikata laifuka a jihar Legas na shekarar 2015.

Alkalin kotun T. O Shomade ya bayar da belin wacce ake tuhuma a kan N20,00 tare da daga sauraron karar ya zuwa 28 ga watan nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel