Duk adawar mai adawa da hassadar mai hassada sai ya yaba mana a kan tsaro - Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar duk adawar mutum da kiyayyar sa da gwamnatin sa zai yaba masa a kan tsaro
- Buhari ya furta wadannan kalamai yayin ziyarar da ya kai jihar Taraba bayan harin da aka kai wa makiyaya a mambila
- Buhari ya ce tun bayan hawansa mulki gwamnatin sa ta mayar da hankali a kan yaki da aiyukan ta'addanci
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce duk kiyayyar mai kiyayya da hassadar mai hassada zai yabawa kokarin gwamnatinsa a kan harkar tsaro.
Buhari na wadannan kalamai ne yayin ziyarar da ya kai jihar Taraba bayan harin da aka kaiwa makiyaya a Mambila.
Shugaba Buhari ya nuna rashin jin dadinsa bisa samun yawaitar rikici tsakanin makiyaya da manoma tare da bayyana aniyar gwamnatinsa na cigaba da yaki da aiyukan ta'addanci a fadin kasar nan.
Kazalika ya jajantawa mutanen jihar Taraba bisa asarar rayuka da dukiyoyin da su ka yi sakamakon rigingimun da su ka afku a jihar musamman na kwanannan.
DUBA WANNAN: Ya rasa ransa a rububin kwasar kudin da dan majalisa ya watsa
A yayin da ya kai jihar, jiya Litinin, shugaba Buhari ya gana sarakunan gargajiya da wakilan makiyaya da manoma da manyan jami'an tsaro da gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Darius Ishaku domin jin ta bakinsu a kan rigingimun dake faruwa jihar.
Buhari ya bayyana cewar ya kai ziyarar ne takamaimai domin ganawa da Shugabannin jama'ar jihar domin yi masu jaje tare da kara jaddada masu aniyar gwamnati na tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'umma.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng