An kama wani ma’aikacin shari’a yana luwadi da dan shekaru 13 a harabar kotu
Jami’an NSCD sun kama wani ma’aikacin kotu mai shekaru 42, Yusuf Adamu, daga a jigawa a kan zargin luwadi da wani karami yaro mai shekaru 13.
Mai laifin ya kasance ma’aikacin kotun Majistare na Birninkudu, sannan kuma ya aikata wannan mummunar aikin ne a harabar kotun da daddare.
Kwamandar rundunar hukumar ta NSCDC dake birnin Dutse, Muhammed Durmin Iya, ya sanar da hakan ne a ranar Litinin bayan ya gabatar da wanda ake zargi ga ‘yan jarida.
An kama wanda ake zargin ne a harabar kotun majistare dake Birninkudu a lokacin da ya ke yunkurin jan yaron zuwa cikin kotun domin aikata masha'an.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta amince da biyan N650bn na tallafin man fetur
Mai laifin ya amsa laifinsa tare da cewa shi ya koyawa yaron wannan mumunan hali sannan kuma wannan shine karo na hudu da suke aikata hakan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng