Mata 12m ake yiwa auren wuri a duk shekara - UNICEF

Mata 12m ake yiwa auren wuri a duk shekara - UNICEF

A wata sabuwar kididdigar bincike da majalisar dinkin duniya reshen UNICEF ta fitar a ranar Talatar da ta gabata ta bayyana cewa, akwai kimanin mata miliyan 12 da ake yiwa auren wuri a duk shekara a fadin duniyar nan.

Wannan sabuwar kididdiga ta bayyana yadda adadin ya sauka da kaso 15 cikin 100 a shekaru goma da suka gabata, daga mace daya cikin hudu zuwa mace daya cikin kowace biyar.

UNICEF ta yi gargadin cewa, idan wannan lamari ya ci gaba da tafiya akan haka, zuwa shekarar 2031 za a samu kimanin mata miliyan 150 a fadin duniya da aka yiwa auren wuri wandanda shekarun su ba su kai 18 ba.

Binciken ya kuma tabbatar da cewa, adadin mata da ake yiwa auren wuri a Kudancin nahiyyar Asia ya ragu daga kaso 50 zuwa 30 cikin 100 a halin yanzu.

KARANTA KUMA: Nau'ikan Cututtuka 5 da Hawan Jini ke haifar wa

Legit.ng ta fahimci cewa, akwai kimanin mata miliyan 650 da suke raye a duniya a halin yanzu da suka yi aure tun ba su wuci shekaru 18 da haihuwa.

Majalisar dinkin duniya ta fara shirye-shiryen kawo karshen yiwa mata auren wuri daga yanzu zuwa shekarar 2030.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng