Iska mai karfi ta yi sanadiyyar jefa miliyoyin jama'a cikin tashin hankali
- Wata iska da ba'a taba yin irinta ba tun baya da shekaru 30 da suka wuce a Amurka ta yi sanadiyyar jefa miliyoyin mutane cikin duhu
- A lokacin da iskar ta taso babu alamar iska ko hadari a duk yankunan da abin ya shafa
- Iskar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 9, ciki kuwa harda wasu yara kanana guda biyu da bishiyoyi suka fado musu akai
Wata iska da ba'a taba yin irinta ba tun baya da shekaru 30 da suka wuce a Amurka ta yi sanadiyyar jefa miliyoyin mutane cikin duhu, sannan kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutane tare da lalata gidaje da dama a yankin arewa maso gabas na kasar ta Amurka.
DUBA WANNAN: Karin Albashi: Muna yin iya bakin kokarin mu domin ganin an samu karin albashi - Shugaban Kungiyar Kwadago
A yanzu haka sama da mutane miliyan daya ne suke zaune a ciki duhu a sakamakon rashin wutar lantarki a wasu wurare a yankin arewa maso gabas na kasar ta Amurka, a dai dai lokacin da ma'aikatan wutar lantarkin suke ta faman aiki ba kakkautawa domin ganin sun gyara wutar, wanda wata iska mai karfin gaske da ta shafi yankin kwanaki uku da suka gabata.
A lokacin da iskar ta taso babu alamar iska ko hadari a duk yankunan da abin ya shafa, iskar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 9, ciki kuwa harda wasu yara kanana guda biyu da bishiyoyi suka fado musu akai.
A yanzu haka dai yankuna da dama a kasar suna fuskantar kalubale na zama cikin duhu dalilin dauke wuta, wanda iskar ta yi sanadi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng