Jerin jahohi 11sun sake karbar bashin Naira 16.1 biliyan daga gwamnatin tarayya

Jerin jahohi 11sun sake karbar bashin Naira 16.1 biliyan daga gwamnatin tarayya

A wani labari da muke samu yana nuni ne da cewa akalla jahohi sha daya daga cikin ashirin da ukku ne da a baya gwamnatin tarayya ta ba lamunin karbar tallafin bashi domin inganta kasafin kudin su sun anshi kudaden da suka kai Naira biliyan 16.1 zuwa watan Janairun shekarar nan da muke ciki.

Mun samu hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa mataimakin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai watau Laolu Akande ya fitar dauke da sa hannun sa ya kuma rabawa manema labarai.

Jerin jahohi 11sun sake karbar bashin Naira 16.1 biliyan daga gwamnatin tarayya
Jerin jahohi 11sun sake karbar bashin Naira 16.1 biliyan daga gwamnatin tarayya

KU KARANTA: Yan sanda, jami'an NSCDC za su ba makarantun kwana na Arewa maso gabas kariya

Legit.ng dai ta samu cewa a cikin sanarwar da ya fitar, Mista Akande bai lissafa sunayen jahohin da suka anfana da kudaden ba amma ya tabbatar da cewa sauran jahohin 12 suma za su karbi kason su nan ba da dadewa ba.

A wani labarin kuma, Yayin da zaben shekarar 2019 ke da da kara karatowa, uwargidan shugaba Muhammadu Buhari watau Aisha Buhari a jiya Litinin ta yi wani gagarumin taro da shugabannin mata na jam'iyyar APC mai mulki su 36 daga dukkan jahohin kasar nan.

Haka ma dai mun samu cewa cikin matan da suka halarci taron hadda uwargidan mataimakin shugaban kasar Najeriya Dolapo Osinbajoda kuma mataimakiyar shugabar mata ta jam'iyyar Tina Adike tare kuma da matar gwamnan jihar Sokoto Maryam Tambuwal.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng