Rundunar sojin kasar Jamus ta yi alkawarin taimakawa rundunar sojin Najeriya wajen yaki da ta’adanci

Rundunar sojin kasar Jamus ta yi alkawarin taimakawa rundunar sojin Najeriya wajen yaki da ta’adanci

- Tawagar rundunar sojin kasar jamus sun kawo wa Najeriya ziyara

- Sojojin kasar Jamus ta yi alkawarin taimakawa rundunar sojin Najeriya wajen yaki da ta’adanci

Rundunar sojojin kasar Jamus da suka ziyarci GOC na 81 Division na rundunar sojojin Najeriya dake Victoria Island, a jihar Lagos, ya bayyana damuwar sa akan kalubalen da Najeriya ke fuskanta a fannin tsaro, musamman matsalar ‘yan ta’adda, masu fasa bututun mai da masu garkuwa da mutane.

Shugaban rundunar sojin kasar Jamus, Kanal Thorsten Schutz, ya fadawa manema labaru cewa sun kawo wa GOC rundunar 81 Division, Manjo Janar Emabong Udoh, ziyara ne saboda sannin yadda suke fama da rikicin yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Kanal Schutz yace, rahotannin dake suke samu daga kafofin watsa labaru akan Najeriya, ya nuna kasar na fuskanatar kalubale a fannin tsaro da kuma tattalin arziki musamman a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Rundunar sojin kasar Jamus sunyi alkawarin taimakawa rundunar sojin Najeriya wajen yaki da ta’adanci
Rundunar sojin kasar Jamus sunyi alkawarin taimakawa rundunar sojin Najeriya wajen yaki da ta’adanci

Amma zuwan shi Najeriya ya ga kasar ta na cikin zaman lafiya sabanin rahotannin da ake yadawa a kafofin watsa labaru.

KU KARANTA : Masu bincike sun gano sabuwar maganin cutar kanjamau

Kanal Schutz, ya yaba da kokarin da jam’ian tsaro Najeriya suke yi wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta a fannin tsaro.

Manjo Janar Emabong Udoh, ya bayyana farincikin sa da ziyarar da sojojin Jamus suka kawo wa rudunar sojin Najeriya, kuma ya bukace da su yawaita irin wannan ziyara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng