Nigerian news All categories All tags
Saudiyya ta kare kan ta kan shiga yakin Yaman

Saudiyya ta kare kan ta kan shiga yakin Yaman

- Saudiya ta kare kanta akan suka da ta ke she saboda shiga yakin kasar Yaman

- Saudiyya ta ce burin ta shine kawo karshen masu tada kayar baya a kasar Yaman da sauran kasashen Larabawa baki daya

Ministan harkokin kasar waje na Saudiyya, Adel al Jubeir, ya kare matakin shiga yakin kasar Yaman da Saudiyya ta yi.

Adel al Jubeir, ya ce ‘yan tawayen kabilar Houthi suka kasar Yaman halin da ta ke cikin a yanzu.

Al-jubeir ya zargi 'yan shi'a na kabilar Houthi na Yaman, da tilastawa yara masu shekaru Tara shiga yakin da suke yi da gwamnati, da kuma yin awon gaba kayan agajin da ake kai wa faraen hula.

Jami’an Majalissar Dinkin Duniya sun dora alhakin fararen hula da ake kashewa a Yaman akan hare haren da kasar Saudiya ke jagoranta ta sama.

Saudiyya ta kare kan ta kan shiga yakin Yaman

Saudiyya ta kare kan ta kan shiga yakin Yaman

Da yake jawabi gabannin kai wata ziyara kasar Bahrain, tare da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, Al-Jubeir, ya ce gwamnatin Saudiyya na kokarin ganin an magance matsalar masu tada kayar baya, da 'yan tawayen da kasashen labarawa ke fama da su a halin yanzu.

KU KARANTA : Masu bincike sun gano sabuwar maganin cutar kanjamau

Kasar Saudiyya dai ta na shan suka kan matakin shiga yakin cikin gida na kasar Yaman, inda masu sharhi kan al'amuran gabas ta tsakiya ke ganin kamata ya yi Saudiya ta zama mai sulhu a duk lokacin da rikici ya barke a yankin kasashen labarawa bai wai ta tsunduma cikin rikicin ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel