Bikin shekaru 81 a duniya: Babbar nadama ta a rayuwa - Obasanjo

Bikin shekaru 81 a duniya: Babbar nadama ta a rayuwa - Obasanjo

Tsoho shugaban kasar Najeriya Cif Olushegun Obasanjo ya yi karin haske da sharhi a game da yadda rayuwar sa ta kasance a baya tun bayan haihuwar sa kimanin shekaru 81 kenan inda ya bayyana cewa daya daga cikin abunda yake nadama a rayuwar sa bai wuce yadda iyayen sa ba suyi tsawon rai ba.

Tsohon shugaban kasar wanda shine na farko na farar hula a wannan jamhuriyar ya bayyana cewa a kullum ya tuna cewa iyayen sa ba suyi tsawon rai ba dan cin gajiyar sa sai ran sa yayi matukar baci.

Bikin shekaru 81 a duniya: Babbar nadama ta a rayuwa - Obasanjo
Bikin shekaru 81 a duniya: Babbar nadama ta a rayuwa - Obasanjo

KU KARANTA: PDP za ta tsayar da Dankwambo magajin Buhari

Legit.ng ta samu cewa shugaban kasar ya yi wannan kalamin ne yayin da ake jawabi ga wasu jiga-jigan yan kasar ciki kuwa hadda 'yan uwan sa da kuma abokan arzikin sa da suka je domin taya shi muranan zagayowar ranar haihuwar sa a dakin karatun sa dake a garin Abeokuta.

A wani labarin kuma, Kwamishinan raya karkara da jin dadin kauyuka na jihar Kano Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso a jiya ya zargi tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da yin kunnen uwar shegu da gayyatar da kwamitin sulhu na jam'iyyar APC karkashin jagorancin Cif Bola Tinubu yayi masa.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a garin Kano yayin da yake zantawa da manema labarai amma sai dai tuni makusantan tsohon gwamnan suka karyata shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng