Kano ba sulhu: Kwankwaso yayi fatali da kiran kwamitin sasanci na Tinubu
Kwamishinan raya karkara da jin dadin kauyuka na jihar Kano Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso a jiya ya zargi tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da yin kunnen uwar shegu da gayyatar da kwamitin sulhu na jam'iyyar APC karkashin jagorancin Cif Bola Tinubu yayi masa.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a garin Kano yayin da yake zantawa da manema labarai amma sai dai tuni makusantan tsohon gwamnan suka karyata shi.
KU KARANTA: Bikin diyar Ganduje: Dakta Gumi ya yi tofin Allah-tsine ga shugabannin Arewa
Legit.ng dai ta samu cewa kwamishinan ya bayyana cewa Cif Tinubu din ya gayyaci Sanata Kwankwaso din ya zuwa wani zaman sulhu da za suyi da gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje jim kadan bayan kammala daurin auren diyasar sa a ranar Asabar din da ta gaba ta amma sai ya ki zuwa.
A wani labarin da muke samu kuma, Wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun yi wani taron sirri a daren ranar Lahadi a can garin Gombe bayan kamma taron majalisar zartarwar jam'iyyar da ya gudana a gidan gwamnatin jihar ta Gombe.
Kamar dai yadda muka samu da majiyoyin mu kuma, gwamnonin sun tattauna ne a kan yadda za su fito da gwamnan jihar ta Gombe da yanzu haka yake kare wa'adin mulkin sa a shekarar 2019 domin ya gwabza da shugaba Buhari.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng