Likita ya karya hakarkarin jariri a kokarin karbar haihuwa

Likita ya karya hakarkarin jariri a kokarin karbar haihuwa

- Wata mata mai shekaru 21 ta zargi likita a wani asibiti, Moses Kotane, da da karya hakarkarin jaririnta

- Uwar ta bayyana cewar ba a bari tayi ido hudu da jaririyar da ta haifa ba sai bayan kwana guda

- Kakakin ma'aikatar lafiya na yankin arewa maso yamma, Tebogo Lekgethwane, ya ce suna gudanar da bincike a kan zargin

Wata mata, Leobogang Setshotloe, ta zargi likitan asibitin Moses Kotane, da karya hakarkarin jaririnta yayin karbar haihuwa.

Uwar 'yar kasar Afrika ta kudu ta bayyana cewar hukumomin asibitin sun hana ta ganin jaririyar ta na tsawon kwana guda, kafin daga bisani ta fuskanci cewar hakarkarin jariririyar ta a karye yake.

Likita ya karya hakarkarin jariri a kokarin karbar haihuwa
Likita ya karya hakarkarin jariri a kokarin karbar haihuwa

Setshotloe ta bayyanawa jaridar Sun cewar asibitin sun ci amanar ta.

"Na tambayi ma'aikaciyar asibitin abinda ya sa hakarkarin jariririyar take a karye, amma sai kawai ta ce min likitan ya yi nadamar abinda ya faru, wai kuskure ne," a cewar Setshotloe.

Sannan ta cigaba da cewa "ban yarda da abin da ta fadamin ba don kamata ya yi likitan ya sanar da ni da kan sa, sannan ya nemi gafara a wuri na."

DUBA WANNAN: Halin da Najeriya zata shiga muddin shugaba Buhari bai koma mulki ba - Gwamna Sani Bello

Uwar ta bayyana cewar abinda ya faru ya matukar bata mata rai, saboda haka tana bukatar likitan da hukumar asibitin su nemi afuwar ta.

Wani kawun matar, Jacob Kobedi, ya ce ba zasu yarda da abin da likitan ya aikata ba, a saboda haka zasu bi hakkin su.

Kakakin ma'aikatar lafiya a yankin arewa maso yamma na kasar Afrika ta kudu, Tebogo Lekgethwane, ya ce suna gudanar da bincike a kan wannan zargi da matar ke yiwa likitan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng