Yanzu-yanzu: Bayan kai ziyara Taraba yau, Buhari zai je Benue, Yobe, Zamfara da Ribas kwananki masu zuwa – Fadar shugaban kasa
Labara daga fadar shugaban kasa da dumi-dumi ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara dukkan jihohin da aka samu matsalan kasha-kashe ko hatsaniya a fadin tarayya.
Fadar shugaban kasa ta bayyana hakan ne a shafin sada ra’ayin da zumuntarta na Tuwita da safiyar yau cewa shugaba Buhari ya amsa kiran al’umma.
Jawabin yace: “Bayan dubi cikin rahotannin, shugaban kasa ya yanke shawara kai ziyaran jaje daya yau inda zai je Taraba, sannan ya kai ziyara jihar Benuem Yobe da RIbas.”
Zaku tuna cewa mun kawo muku rahoton cewa bias kan kashe-kashe da ya faru a jihar Taraba karshen makon da ya gabata, ana sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyarar ban mamaki jihar Taraba yau.
KU KARANTA: Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Taraba yau
Jaridar Vanguard ta bada wannan rahoto ne da safiyar yau Litinin, 5 ga watan Maris, 2018. Wannan labari na fitowa ne bayan ana sa ran shugaban kasan zai je kasar Ghana domin halartan taron murnan zagayowar ranan samun yanzin kasar shekari 61.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng