Sojojin Najeriya sun koka akan yadda aka cigaba da sa su yin aikin ‘yasanda

Sojojin Najeriya sun koka akan yadda aka cigaba da sa su yin aikin ‘yasanda

- Manyan sojojin Najeriya sun yi kira da gwamnatin tarayya ta kara wa rundunar 'yasanda Najeriya ma'aikata

- Sojojin Najeriya sun ce aikin warware matsalolin cikin gida na 'yansanda ne ba na sojoji ba

Rundunar sojin Najeriya ta ce, cigaba da sa su yin aikin ‘yansanda a jihohi 32 a fadin kasar, yana ci musu tuwo a kwarya.

A lokacin da aka gudanar da taron manyan jami’an sojojin karo na 40 a Kwalejin Sojoji dake Jaji a jihar Kaduna, manyan jami'an sojojin Najeriya sun yi kira da gwamnatin tarayya ta kara wa rundunar 'yasandan Najeriya ma'aikata.

Sojoji sun ce kara wa rundunar yansadar Najeriya ma'aikata da yi musu horon da zai sa su iya aikin su kamar yadda yakamata ya zama dole.

Sojojin Najeriya sun koka akan yadda aka cigaba da sa su yin aikin ‘yasanda
Sojojin Najeriya sun koka akan yadda aka cigaba da sa su yin aikin ‘yasanda

Sun ce ba dai-dai bane a ce kasa kamar Najeriya mai yawan mutane sama da miliyan 182 ta na da jami’an ‘yansanda kasa da 40,000.

KU KARANTA : Jam'iyyar APC ta lashe kananan Hukumomi 7 a zaben Jihar Edo

Sojojin sun ce aikin su shine kare iyakokin kasar, ba wai war-ware riginginmu cikin gida ba wanda shine aikin ‘yasanda a kasashen da suka cigaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng