Sai Buhari ya fara canza kansa da na mukarrabansa kafin aga canji a kasar – Bashir Tofa
- Bashir Tofa ya soki kudirin 'Daga kaina canji zai fara' da gwamnatin tarayya ta kaddamar
- Tofa ya ce sai shugabannin sun fara canza halayen su kafin kafin sauran al’ummar kasar su canza na su hakayen
Sanannen tsohon dan siyasa a jihar Kano kuma attajirin dan kasuwa, Alhaji Bashir Tofa, ya soki shirin wayar da kan al’ummar Najeriya mai taken ‘Change Begins with me’ Daga kaina canji zai fara.
Alhaji Bashir Tofa, ya ce, kamata ya yi a fara ganin canji daga kan Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da kan mukarraban sa tukunna kafin sauran al’ummar kasar.
‘‘Kamata ya yi shugabanni su fara canza halayyar su da wadanda ke kewaye da su kafin halayyar wadanda suke shugaban ta ya canza, in bahaka kamfen din ‘Daga kaina canji zai fara’ da gwamnatin tarayya ta kaddamar zai zama shiririta," Inji Bashir Tofa.
KU KARANTA : Babu inda kananan yara suka kada zabe a Kano – INEC ta wanke Kano
Ya kara da cewa wannan shiri ba zai taba yin tasiri ba har sai al'ummar kasar sun ga canji a cikin aljihun su, maimakon a cikin aljihunn wasu tsirarun mutane.
Alhaji BahsirTofa, ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya halarci taron kaddamar da shirin 'Change begin with me' Daga kaina cin zai fara a dakin taro na gidan Gwamnatin Jihar Kano.
Danna wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng