'Yan majalisar Najeriya sun shirya yin fito na fito da Buhari akan kin amincewa da kafa rundunar 'Peace Corps'

'Yan majalisar Najeriya sun shirya yin fito na fito da Buhari akan kin amincewa da kafa rundunar 'Peace Corps'

- 'Yan majalisar Najeriya sun shriya yin fito na fito da Buhari akan kin amincewa da kafa rundunar 'Peace Corps'

- Wasu 'yan majalissar dattijai sun ce kafa rundunar Peace Corps zai gyara siyasar su kafin zabe mai zuwa

Legit.ng ta samu rahoton cewa yan majalissar wakillai sun shirya kalubalanatar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a cikin wannan makon akan kin rattaba hannu a kudirin kafa rundunar ‘Peace Corps’

Wasu ‘yan majalissar Najeriya sun fadawa manema labaru cewa za su dauki mataki akan kin amincewa da rattaba hannu a kudirin kafa rundunar ‘Peace Corps’ da Buhari yayi, saboda irin kokarin da suke yi wajen tatance hukumar a shekarar da ta gabata.

'Yan majalisar Najeriya sun shriya yin fito na fito da Buhari akan kin amincewa da kafa hukumar Peace Corps
'Yan majalisar Najeriya sun shriya yin fito na fito da Buhari akan kin amincewa da kafa hukumar Peace Corps

‘Yan majalissa dattijai da dama sun bayyana takaicin su akan wannan al’amari, inda mafi akasarin su suka ce, kafa hukumar zai gyara siyasar su kafin zabe mai zuwa.

KU KARANTA : Rundunar 'yan sandan Zamfara ta dakile yunkurin kai hari a Anka

Mai magana da yawun bakin majalissar dattijai, Sanata Sabi Abdullahi, yace majalissar dattijai za ta yi amfani da karfin da dokar kasa ta bata wajen kafa hukumar Peace Corps idan shugaban kasa ya kara kin rattaba hannu a kudirin kafa rundunar ‘Peace Corps’.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng