Ba’a mugun sarki, sar mugun bafade: Don bukatar kashin kai wasu Kwamishinoni na amfani da tsafe tafe wajen juya gwamnansu
Asiri ya tonu game da yadda wasu Kwamishinoni a jihar Osun ke yi ma gwamnansu, Rauf Aregbesola asiri don su samu biyan bukata game da wata alfarma da suke nema a wajensa, inji rahoton Daily Trust.
Kwamishiniyar al’amuran mata da kananan yara a jihar, Alhaja Latifat Abiodun ce ta bayyana haka a yayin wani taron kungiyar wayar da kan musulmai game da al’amuran siyasa, MUPAF, a ranar Lahadi, 4 ga watan Maris a garin Osogbo.
KU KARANTA Fadar shugaban kasa tayi magana a kan satar 'yan matan Dapchi, takarar Buhari
Latifat tace gwamna Rauf ya yi iya kokarinsa a mulkin jihar Osun, inda tace idan mutanen jihar sun ga wata matsala, toh su sani ba daga gareshi bane, daga mukarrabansa ne, saboda a cewarta ta kai ga wasu daga cikin kwamishinoninsa na yi masa asiri da tsafe tsafe don ya biya musu bukatar kashin kai.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Latifat tana cewa: “Kada ku da laifin gwamna, face hadimansa, da dama daga cikinsu na yi masa asiri ne, musamman a zangon mulkinsa na farko, har ta kai ga sun gina gunkinsa, inda ta nan suke juya shi.
“Wata rana, wani daga cikinsu na son ganwa da gwamna, amam kafin nan sai ya ruga bandaki a guje, fitowarsa keda wuya, sai ya jami’an tsaro suka tare shi, suka tambaye shi menene a jikinsa, ana dagawa sai ga layu dayawa a jikinsa.” Inji ta.
Sai dai a nasa jawabin, Kwamishinan ilimi na jihar, Omotunde Young, wanda ya wakilci gwamnan jihar ya nemi afuwan mahalarta taron a madadin gwamnan game da rashin samun damar halarta kamar yadda ya yi alkawari tun a baya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng