Kunnenka nawa? Karanta yadda aka kwashi Amarya Fatima Ganduje zuwa dakin mijinta (Hotuna

Kunnenka nawa? Karanta yadda aka kwashi Amarya Fatima Ganduje zuwa dakin mijinta (Hotuna

Tabbas, masu kudi na shagalinsu, a yayin da wasu ma’aurata ke karyar daukan amarya a cikin manyan matoci, su kuma a kauyuka su dauki amarya a kan jaki, sai ga shi Fatima Ganduje ta fita daban.

A ranar Lahadi, 4 ga watan Maris ne dai, aka kai diyar gwamnan jihar Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje da aka daura aurenta a ranar Asabar, Fatima Ganduje da Angon Idris AJimobi, yaron gwamnan jihar Oyo, dakinta.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa tayi magana a kan satar 'yan matan Dapchi, takarar Buhari

Kunnenka nawa? Karanta yadda aka kwashi Amarya Fatima Ganduje zuwa akin mijinta (Hotuna
Ma'aurata

Sai dai irin wannan daukan Amarya ba kasafai aka saba ganinsa ba, idan ba wai a wajen masu hannu da shuni bane, inda aka dauki wannan Amarya a cikin jirgin sama, jirgin ma ba wai irin na yan kasuwa ba, jirgin shata, wanda ake yi ma suna da ‘Private Jet.”

Kunnenka nawa? Karanta yadda aka kwashi Amarya Fatima Ganduje zuwa akin mijinta (Hotuna
Amarya

A Hotunan da Legit.ng ta gano, wasu tsala tsalan yan mata su hudu ne suka fara rako diyar gwamnan har cikin filin jirgin saman, inda suka mikata ga Angonta Idris, wanda yake tsaye tana dakon jiranta, daga nan shi kuma ya rike mata hannu zuwa cikin jirgin dake jiransu, sai Ibadan, dakin Amarya.

Kunnenka nawa? Karanta yadda aka kwashi Amarya Fatima Ganduje zuwa akin mijinta (Hotuna
Sarki tare da Ma'aurata

Idan za’a tuna, wannan taro ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Bukola Saraki, Asiwaju Ahmad Bola Tinubu, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi, gwamnoni da dama, da kuma yan kasuwa, Sanatoci, Yan majalisu da sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng