Manyan yan siyasa daga Adamawa sun dawo bayanmu - SDP

Manyan yan siyasa daga Adamawa sun dawo bayanmu - SDP

- Jam’iyyar Social Democratic Party ta ce tana sanya ran samun karin yan siyasa kafin zaben 2019

- Sakataren jam’iyyar na kasa yayi ikirarin cewa gwamnoni biyar da sanatoci ashirin zasu koma jam’iyyar kwanan nan

- Ya kara da cewa jam’iyyar na sa ran dawowar mambobin majalisar wakilai da masu fada a ji a harkar siyasa

A ranar Lahadi, 4 ga watan Maris, babban sakataren jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Alfa Mohammed, ya bayyana cewa jam’iyyar na sa ran dawowar gwamnoni biyar da sanatoci ashiri, da kuma yan majalisar wakilai da dama jam’iyyar kwannan nan.

Kakakin jam’iyyar, wanda yayi Magana a Minna, jihar Niger, ya kuma bayyana cewa zai tabbatar a nan da makonni uku idan tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar zai koma jam’iyyar ko akasin haka, jaridar Punch ta ruwaito.

Manyan yan siyasa daga Adamawa sun dawo bayanmu - SDP
Manyan yan siyasa daga Adamawa sun dawo bayanmu - SDP

Mohammed yace kimanin gwamnoni biyar suka nuna ra’ayin dawowa jam’iyyar sannan kuma kwanan nan zasu dawo jam’iyyarkwanna nan tare da al’umma 50 wanda tuni sun dawo jam’iyyar.

A halin da ake ciki Jam’iyyar PDP ta taya tsohon shugaba Obasanjo murna yayinda ya cika shekaru 81 a ranar Litinin, 5 ga watan Maris.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta saki ta hannun kakakinta, Kola Ologbondiyan a ranar Lahadi, 4 ga watan Maris tace har yanzu tana alfahari da tsohon shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari bata da karfin kare yan Najeriya - Suswam

Ta bayyana cewa Obasanjo ya ba da gaggfarumin gudunmawa wajen zaman lafiya da ci gaban kasashen duniya, musamman a yankin nahiyar Afrika, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel