An kashe muta 20, an sace shanaye 300 a sabon rikicin kabilanci da ya balle a jihar Taraba
- Sabon rikici ya balle tsaknain makiyaya da mazauna Leme a karamar hukumar Sadauna dake jihar Taraba
- An rahoto cewa an kashe mutane 20, 12 sun ji rauni yayinda aka sace shanaye 300
- Mazauna yankin sunyi ikirarin barin gidajesu bayan harin
Wani sabon rikicin kabilanci da ya balle a Mambilla Plateau karamar hukumar Sardauna dake jihar Taraba a ran ar Lahadi, 4 ga watan Maris yayi sanadiyan mutuwar mutane ashiri, yayinda aka sace shanaye guda dari uku.
Wani mazaunin garin wanda ya tsere a lokacin rikicin, Saadu Magoggo, ya bayyana cewa wata kungiya ta Mambilla Militia ta kashe yan uwansa guda biyu a ranar Asabar sannan kuma an sace dabbobinsu , jaridar Vangurd ta ruwaito.
Wani shugaban Fulani, Ahmadu Nguroje, ya ce akalla mutane 20 ake ganin sun mutu, anyi sace-sace a gidaje, shaguna sannan kuma an kona su zuwa toka a hanyar Tapare da Yerimaru dake karamar hukumar Sardauna na jihar Taraba. “Kimanin mutane 12 ma sun ji rauni suka kwance a asibiti a Gembu.”
Da yake maida martini ga rikicin, Gwamna Darius Ishaku, wanda yayi Magana ta babban mai bashi shawara akan harkokin jama’a, Emmanuel Bello, ya ce: “duk wanda ya kashe wani, daga ko wani addini ko kabila, mai laifi ne; imam ya fito daga yankin Mambilla ko kudancin Taraba koma daga ko wani yanki na jihar. Sannan kuma zamuyi maganinsu a matsayin masu laifi.
KU KARANTA KUMA: PDP ta taya Obasanjo murnar cika shekaru 81; ta ce yana daya daga cikin shugabannin da suka yi aiki sosai a Najeriya
“Muna kokarin ganin an sasanta rikicin tare da dawo da zaman lafiya a tsakannin dukannin kabilu a jihar.”
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng