Buhari zai hallarci bikin cikar kasar Ghana shekaru 61
- A ranar Talata, 6 ga watan Maris, kasar Ghana ke murnar cika shekaru 61 da samun 'yanci
- Shugaba Buhari zai bar gida Najeriya zuwa birnin Accra na kasar Ghana domin halartar shagalin bikin
- Buhari ne kadai shugaban kasa da kasar ta Ghana ta gayyata don ya halarci taron
Shugaba Muhammadu Buhari zai bar gida Najeriya a gobe Litinin domin halartar taron bukukuwan cikar kasar Ghana shekaru 61 da samun 'yanci.
Shugaba Buhari zai sauka a Accra, babban birnin kasar Ghana, a gobe domin jerin bukukuwan da za a gabatar ranar Talata, 6 ga wata.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar da wannan sanarwa. Adesina ya bayyana cewar, shugaba Buhari ya kafa tarihi a matsayin shugaban kasa daya tilo da kasar Ghana ta gayyata domin halartar taron, kuma mutum na biyu, bayan shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, da zasu yi jawabi wurin taron.
KU KARANTA: Ganduje ya bawa Ajimobi mamaki bayan ya nemi a biya N50,000 a matsayin sadakin auren diyar sa
Buhari zai yi amfani da damar jawabinsa wajen yin waiwaye a kan yadda kasashen Najeriya da Ghana su ka dade su na zumunta tare da jaddada imanin Najeriya a kulla kawance tsakanin kasashen Afrika ta yamma, da ma nahiyar Afrika bakidaya.
A tawagar shugaba Buhari akwai; Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama, mai ba shi shawara a kan har tsaro, Babagana Monguno.
Shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya a ranar ta Talata bayan kammala taron.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng