Wuta ta kone su bayan sun fasa bututu domin satar danyen man fetur

Wuta ta kone su bayan sun fasa bututu domin satar danyen man fetur

- Mutane biyar sun rasa ransu bayan fasa bututu domin satar danyen man fetur a jihar Bayelsa

- An samu gawar wadanda suka mutun ranar 25 ga watan Fabrairu, 2018, a karamar hukumar Ekeremor

- Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Bayelsa, Mista Asinim Butswat, ya ce ba sanar da su afkuwar lamarin a hukumnan ce ba

Sa'a ta karewa wasu mutane biyar bayan sun yi amfani da wani sindari mai fashewa domin fasa bututun danyen man fetur a jihar Bayelsa.

Majiyar jaridar Vanguard ta rawaito cewar mazauna wani kauye dake kusa da bututun ne su ka tsinci gawar mutanen ranar 25 ga watan Fabrairu, 2018, a surkukin Azagbene dake karamar hukumar Ekeremor.

Wuta ta kone su bayan sun fasa bututu domin satar danyen man fetur
Wuta ta kone su bayan sun fasa bututu domin satar danyen man fetur

Mutanen sun yi kokarin fasa bututun ne da sindarin "Dynamite" mai fashewa kamar yadda mutanen kusa da wurin su ka tabbatar da cewar sun ji karar fashewar sindarin da sanyin safiya kafin daga bisani su hangi tashin wuta na ci ganga-ganga.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tayi magana a kan satar 'yan matan Dapchi, takarar Buhari

Sai dai bayan mutanen kauyen sun isa wurin sai su ka iske gawar mutane biyu yayin da su ka samu ragowar mutane uku cikin mawuyacin hali.

Kakakin hukumar 'yan sanda jihar Bayelsa Mista Asinim Butswat ya ce ba a sanar da su afkuwar lamarin ba a hukumance.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng