Mambila: An kashe Fulani 20, an sace musu shanu 300 a sabon rikici a Jigawar Mambila

Mambila: An kashe Fulani 20, an sace musu shanu 300 a sabon rikici a Jigawar Mambila

- AN KASHE KIMANIN MUTN 20 A MAMBILLA, AN KUMA SACE SHANU 300

- A kalla mutun 20 suka rasa rayukan su, sai kuma shanu 300 da aka sace bayan wata hatsaniyar kabilanci da ta barke a Mambilla, a karamar hukumar saurdauna, jihar Plateau

Mambila: An kashe Fulani 20, an sace musu shanu 300 a sabon rikici a Jigawar Mambila
Mambila: An kashe Fulani 20, an sace musu shanu 300 a sabon rikici a Jigawar Mambila

Wani daga cikin 'yan gudun hijirar mai suna Sa'adu Mogoggo, ya bayyana wa manema labarai cewar an kai masa hari a gidansa a kauyen Gembu, in da wasu mutane da ake kira da 'yan kungiyar Mambilla Militia suka kashe masa 'yan uwa guda biyu suka kuma tafi da shanun nasu. Wanda ko a yanzu da muke magana ba'a rufe gawar tasu ba.

Gwamnan jihar, Darius Ishaku, wanda mai ba wa Gwamna shawara ta bangaren harkokin jama' ya wakilta, ya ce duk wanda ya kashe wani ko da dan wace kabila ko addini ne wannan mutun mai laifi ne, za kuma a hukunta su a matsayin masu laifi.

DUBA WANNAN: Hadimi yayi bayanin yadda ya boye biliyan biyar a uwar dakin Jonathan

Mai magana da yawun 'Yan Sanda na jihar, David Misal, ya fadawa manema labarai cewa an tabattar da mutuwar mutun 4 daga ko wanebangare na kabilun. Ya kara da cewa an tura jami'an tsaro don tabbatar da zaman lafiya a yankin duk da daifadi cewa an kama kowa ba.

Bincike dai ya nuna cewa hatsaniyar tafara ne tun ranar Alhamis bayan wata sa in sa da akayi a kan gona zakanin Filani da mutanen garin Yerimaru wanda ya zarce zuwa sauran kauyukan da kusa da su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng