Nigerian news All categories All tags
A bara kasuwancin Tiriliyan 22 jama'ar Najeriya suka yi a cikin gida

A bara kasuwancin Tiriliyan 22 jama'ar Najeriya suka yi a cikin gida

- Habakar tattalin arziki ke kawo ci gaba a kasa da fidda jama'a daga talauci

- An yi kasuwanci na cikin gida da ya zarta na kowacce kasa a Najiyar

- Najeriya na da jama'a akalla miliyan 190

A bara kasuwancin Tiriliyan 22 jama'ar Najeriya suka yi a cikin gida

A bara kasuwancin Tiriliyan 22 jama'ar Najeriya suka yi a cikin gida

Hukumar kididdiga ta kasa a ranar Asabar ta fitar da kididdigar cinikayyar Nijeriya na shekarar 2017, wanda kasar ta karu da N5.5tn a cinikayya daga N17.3tn a 2016, zuwa N23.3tn.

Hukumar a cikin rahoton ta ce yawan kudin da aka shigo dashi ya kai N9.5tn, ya kuma kara da cewa kashi 8.5 cikin 100 kasa da N8.8tn da aka shigo da su a shekara ta 2016. A game da fitarwa rahoton NBS ya nuna abun da aka samu a shekarar 2017, shine N13.59tn, in da aka lura cewa wannan ya karu da kasha 59.47 cikin dari fiye da N8.52tn da aka rubuta a shekara ta 2016.

DUBA WANNAN: An sace amaryar dan majalisa a Katsina

Yawan abun da aka samu shine N2.11tn a Q4, 2017 ya kasance 15.1 a cikin 100 kasa da Q3, 2017 wanda ke N2.48tn, da kasha 8.5 cikin 100, kasa da Q4 a shekarar 2016, wanda ke da N2.3tn. a shekarar 2017 an samu N9.5tn, wanda ya kai kasha 8.5 cikin 100, na karuwar cinikayya da akasa samu sama da yanda ya ke a 2016, a N8.81tn.

Sashen fitar da kaya wajen Nijeriya a cikin kwata na hudu, a cewar rahotanni sunfi dogaro da Man Fetur. Ya ce danyen Man Fetur ya kai Naira N3.25tn a kashi na hudu kuma ya kasance mafi girman jigilar kayayyaki da kasha 83 a cikin dari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel