'Dalilan da suka sa nake so a rataye masu yada kiyayya' - Dan Majalisa

'Dalilan da suka sa nake so a rataye masu yada kiyayya' - Dan Majalisa

- Sani Abdullahi, dan majalisar dattijai ya gabatar da bayani kan kaddamar da dokar Hukumar Harkoki ta kasa, inda ya bayyana dalilin da ya sa aka hada da hukuncin kisa a dokar

- Ya na ganin wannan zaiyi maganin masu kalaman kiyayya a kasar, wanda yanzu haka anyi zama na biyu knan a majalisar dattijan domin tattaunawa akan al’amarin

'Dalilan da suka sa nake so a rataye masu yada kiyayya' - Dan Majalisa
'Dalilan da suka sa nake so a rataye masu yada kiyayya' - Dan Majalisa

Tunda aka fara tattaunawa akan dokar jama’ar Nijeriya na ta kokwanto kan manufar wannan doka. Ana zargin dokar ta samo asali ne bayan maganar da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, wanda ya fadi zagin da yake yiwa shugab Muhammadu Buhari na kokarin juya Nijeriya zuwa Korea ta Arewa.

Sabanin abun da mutane ke tinani dokar ta na bayar da cewa duk mutanen da suke yin kalaman kiyayya za’a kashe su ta hanyar rataya, in ji Kakakin Majalissar Dattijai hukuncin zai hau kan wadan da aka tabbatar da shaida kan cewa sun fadi kalaman na kiyayya wanda ya kaiga wani ya rasa ransa ta dalilin hakan a Babbar Kotun Tarayya.

Abdullahi, ya ce wadanda ke sukar dokar suna yin hakan ne saboda basu taba rasa dangi ba ta hanyar irin wadannan kalaman na kiyayya.

DUBA WANNAN: Dan Najeriya ya bada mamaki a kimiyya a Turai

Ya na da kyau a lura cewa ‘yan kasa suna da damar yin magana yanda suke so, ko fadar ra’ayoyin su basu da laifi. Kada mu mance cewa mutane suna da ‘yancin zama masu son kai ko tsattsauran ra’ayi ya zama dole mu san haka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng