Yadda masu karancin Ilimi da rikicin tsufa ke rike da mukaman iko a kasar nan - Farfesa Nwabueze

Yadda masu karancin Ilimi da rikicin tsufa ke rike da mukaman iko a kasar nan - Farfesa Nwabueze

Cikin fusatuwar rashin daidato a harkokin siyasa da tattalin arzikin Najeriya na wannan lokuta, shugaban masu kishin kasa na kabilar Ibo, Farfesa Ben Nwabueze, ya yi kira kan sauya kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999.

Farfesa Ben ya yi wannan kira akan sauya tsarin shekaru na shiga fagen siyasa daga 70 zuwa kasa da haka domin baiwa kowane dan Najeriya dama ta tsayawa takara ta kujerar shugaban kasa, gwamna da kuma majalisun jihohi da na tarayya.

A sakamakon haka ne, Farfesa ya bayar da misalin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yace ko kadan babu wani kwazo da yake yiwa Najeriya bisa la'akari da rashin karsashi irin matasa da kuma dimaucewa sakamakon shekarun sa da suka ja.

Farfesa Ben Nwabueze
Farfesa Ben Nwabueze

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, a jihar Enugu ne Farfesa ya bayyana fushin sa kan harkokin dake wakana a kasar nan ta Najeriya.

KARANTA KUMA: Kasar Thailand ta zargi shugaba Buhari da laifin rushewar Kamfanonin Shinkafa na Najeriya

A bangaren zurfin karatu da hakokin ilimi na matakin da shugabannin kasar nan suka taka, yace ko kadan basu cancanci jagorantar kasar nan.

Nwabueze ya ci gaba da cewa, sakamakon ilimi yana daya daga cikin ma'auni na tattalin arziki, ya kamata masu jagorantar kasar na su kasance masu zurfi a wannan fanni da kuma karfin jiki sauke nauye-nauyen da ya rataya a wuyan su na jagoranci.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a can jihar Imo ne ajali ya katse hanzarin wani matashi a saman itacen kwakwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng