Da dumi-dumi: An daura auren diyar Ganduje da dan gwamna Ajimobi
An daura aure tsakanin Fatima Abdullahi Umar Ganduje da Idris Abiola Ajimobi a babban masallacin jihar Kano dake fadar mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu a yau Asabar, 3 ga watan Maris, 2018.
Fatima Abdullahi Umar Ganduje diya ce ga gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Shi kuma Idris Ajimobi da ne ga gwamnan jihar Oyo, gwamna AbIola Ajimobi.
Shugaba Muhammadu Buhari tare da mukarraban fadar shugaban kasa sun samu daman halartan wannan taro na musamman.
KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sako iyalan ma'aikacin VOA bayan ya biya N2m
Daga cikin wadanda suka halarci daurin auren sune gwamnoni, Ministoci, shugaban Majalisan dattawa, Bukola Saraki, mambobin majalisan dokokin tarayya, sarakunan gargajiya, Aliko Dangote,Alh Muhammadu Indimi,Alh Aminu Dantata da sauran yan uwa da abokan arziki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng