NNPC tace ba ja da baya kan batun haqo mai a arewa, bayan Boko Haram sun sako ma'aikatan man
- An sako ma'aikatan jami'ar Maiduguri daga Sambisa
- NNPC tace baza ta bar aikin neman mai a arewar ba
- Boko Haram sun hana aiki a yankin dake fama da talauci
Dangane da haqar man tafkin chadi, muna aiki ba dare ba rana kuma muna miqa godiya ga shugaban qasa da ceto wasu daga cikin malamanmu da yayi. "Zamu koma tafkin chadin gadan gadan" yace.
Baru yace "duk da masana'antar man da ta iskar gas ce ta zamo jigo a tattalin arzikin kasar, tana samar da kashi casa'in da biyar na kudin shigar kasar. Babban kalubale da kasar take fuskanta shi ne dogaro da man fetur wanda zai iya wanzar da matsala nan gaba. Yayin assasa bukatar farfado da tattalin arzikin kasar.
Dr. Baru yace "Qarni da yawa da suka shude munyi su a tsanake muna hakar man fetur, noma da kiwo da kuma kasuwanci wanda kowanne bangarorin kasar suka dogara dashi. Amma fa hakan ze cigaba ne in muka qara bunkasa bangaren samarwa na kasar. Yace "matatar man fetur ta kasa tana da alhakin bunkasa kasuwanci, masana'antu da kuma noma da kiwo domin su kaiga wani matsayi a kasar.
DUBA WANNAN: An kashe ma'aikatan UN a jihar Borno
Wannan wani wajibi ne wanda zamu cigaba da kiyayewa. Domin mu tabbatar da kwazonmu, matatar man fetur ta kasa ta fito da wani bangare na renewable energy sources wanda shi ya maida hankali ne ba dan cigaban solar and other renewable energy ba kadai, a'a harda habaka biofuels wanda suke matukar dogaro da albarkatun gona da kuma abincin dabbobi.
Amfanonin wannan bangaren yana da yawa, ya hada da: farfado da bangaren noma da kiwo, samar da aikin yi ga miliyoyin jama'a, samar da wutar lantarki, samar da abincin dabbobi, da kuma sauran by-products da biofuels wanda za'a iya hadasu da man fetur a matatunmu wanda zasu iya taka rawar gani gurin rage shigo da man fetur kasar.
Yace kasar tana bukatar maida hankali gurin kaddamar da gyare gyaren kayan more rayuwa wanda yace basa cikin halin da ya dace. Yace matatar man fetur ta kasa ta dauki matakan magance matsalolin da suke tasowa kwanan nan.
Wasu daga cikin matakan sun hada da deployment da wanzar da '24hours real time fuel war room' domin samar da ingantacce da kuma kasuwar man fetur a baki dayan kasar. Samar da, da kuma siyarda man fetur a duk manyan gidajen man da kuma hadin kai tare da watsa labari ga masu daidaita ko mahukunta a ma'aikatar.
A jawabinshi, wakilin cibiyar kasuwanci, ma'adanai da kuma noma da kiwo na jihar kaduna, Alhaji Tijjani Musa yace hobbasan gwamnatin tarayya gurin rarrabuwar ta fannin habaka tattalin arziki ya fara fito da kyakkyawan sakamako domin a halin yanzu kasar ta dogara da kanta ne ta bangaren rice production.
Ya bada shawarar a maida hankali ga sauran amfanin gona kamar su auduga, gyada,alkama, roba, man ja, da sauransu. Ya kara da cewa wannan ba rashin aikinyi kadai zai magance ba, zai habaka al'amuran kasuwanci da masana'antu
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng