'Yan sandan Najeriya sun kama gaggan barayi da suka addabi jama'a a Abuja

'Yan sandan Najeriya sun kama gaggan barayi da suka addabi jama'a a Abuja

Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya reshen garin Abuja sun sanar da samun nasarar cafke wasu gaggan barayi na mutum 5 da kuma ake zargin wani babban likita ne ke shugabantar su mai suna Dakta Ola Jimade.

Majiyar ta mu dai ta tabbatar mana da cewa akalla kawo yanzu dukkan mutanen dake zargi da satar sun shiga hannun 'yan sandan sai dai shi shugaban na su ne har yanzu ba'a kama shi ba.

'Yan sandan Najeriya sun kama gaggan barayi da suka addabi jama'a a Abuja
'Yan sandan Najeriya sun kama gaggan barayi da suka addabi jama'a a Abuja

KU KARANTA: Hotunan jaririya mai hannu 4 da kafa 3 da aka haifa a Kaduna

Legit.ng ta samu cewa kwamishinan 'yan sandan garin Abuja din mai suna Sadiq Bello ya bayyana cewa wasu masu kishin kasa ne suka kwarmata masu gaggan barayin wanda kuma hakan ya taimakawa su wajen kai samame kafin daga bisani su kama su a maboyar su.

A wani labarin kuma, Majalisar zartaswar Najeriya dake da hada da shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin sa da ministoci da ma wasu manyan ma'aikatan kasar sun amince da ware makudan kudade domin kashewa wajen bayar da tsaro a gabar tekunan Najeriya.

Ministan sufuri na kasar kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Mista Rotimi Amaechi shine ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa gwamnatin ta ware kimanin Naira biliyan 59.86 domin gudanar da aikin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng