Kishi ko Hauka: Wani saurayi ya bankawa gidan budurwar sa wuta

Kishi ko Hauka: Wani saurayi ya bankawa gidan budurwar sa wuta

Wani saurayi mai shekaru 27 a duniya mai suna Ifeanyi Ede a yau dinnan Alhamis ya gurfana a gaban alkalin wata kotun Majistare a garin Abuja, babban birnin Najeriya bisa zargin sa da ake yi na cinnawa gidan budurwar sa wuta.

Da yake bayar da ba'asi, dan sanda mai gabatar da kara mai suna Idowu Lawal kamar yadda muka samu tun farko ya bayyanawa kotun cewa shi dai wanda yake tuhumar ya bankawa gidan budurwar sa mai suna Esther Yahaya dake zaune a garin Kubwa, Abuja wuta a ranar 5 ga watan Maris.

Kishi ko Hauka: Wani saurayi ya bankawa gidan budurwar sa wuta
Kishi ko Hauka: Wani saurayi ya bankawa gidan budurwar sa wuta

KU KARANTA: Kungiyoyi 108 ke son zama jam'iyyu - INEC

Legit.ng haka zalika ta samu cewa sai dai shi wanda ake karar ya musanta zargin da ake yi masa kafin daga bisani alkalin kotun ya bada belin sa kan kudi Naira dubu 150 sannan kuma ya dage shari'ar zuwa ranar 5 ga wata mai kamawa.

A wani labarin kuma, Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci daurin auren Hajiya Fatima diya ga Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kuma Alhaji Idris Abiola, da ga gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi da za ga gudanar gobe a garin Kano.

Mun samu dai cewa an saka daurin auren ne da karfe 12 na rana kuma za'a daura ne a fadar sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel