An ci zarafin dan jarida a harabar majalisar dokokin wannan jihar

An ci zarafin dan jarida a harabar majalisar dokokin wannan jihar

Jami'in dan sandan Najeriya dake shiyyar jihar Akwa ibom a jiya Laraba ya lakadawa wani dan jarida mai suna Mista Samuel Ayara dukan tsiya a harabar majalisar dokokin jihar.

Kamar dai yadda labarin ya zo mana, dan sandan da ya bugi dan jaridar sunan sa Sunday Agada kuma yana aikin gadin dan majalisar jihar ne mai wakiltar karamar hukumar Ikot Abasi mai suna Mista Uduak Udoudo.

An ci zarafin dan jarida a harabar majalisar dokokin wannan jihar
An ci zarafin dan jarida a harabar majalisar dokokin wannan jihar

KU KARANTA: Dalilin da ya sa na ki halartar taron APC - Saraki

Legit.ng ta samu cewa tuni shugabannin kungiyar 'yan jaridar jihar suka fitar da kakkausar sanarwa inda suka yi Allah-wadai da lamarin sannan kuma suka bukaci majalisar ta yi bincike sannan ta kuma hukunta dukkan wanda aka samu da laifi.

A wani labarin kuma, Jami'ar nan mallakin gwamnatin tarayya dake a garin Maiduguri, jihar Borno ta sha alwashin cigaba da hada gwuiwa da ma'aikatar hukumar rukunin kamfunan albarkatun man fetur na kasa watau NNPC wajen binciken da sukeyi na mai a tafkin Chadi.

Wannan dai ikirarin na mahukuntan jami'ar na zuwa ne kwanaki kadan bayan 'yan ta'addan Boko Haram sun sako manyan malaman jami'ar da suka yi garkuwa da su a watannin baya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng