Ana sa ran halartar Buhari bikin diyar gwamna Ganduje da dan Gwamna Ajimobi
Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci daurin auren Hajiya Fatima diya ga Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kuma Alhaji Idris Abiola, da ga gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi da za ga gudanar gobe a garin Kano.
Mun samu dai cewa an saka daurin auren ne da karfe 12 na rana kuma za'a daura ne a fadar sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
KU KARANTA: Dapch: Barayin 'yan matan sun tuntube ni - Mama Boko Haram
Legit.ng dai ta samu cewa ana sa ran garin na Kano ya cika makil da manyan baki da abokan arziki daga kowa bangare na kasar nan kama daga gwamnoni, ministoci da ma 'yan majalisun tarayya da na jiha.
A wani labarin kuma, Wani saurayi mai shekaru 27 a duniya mai suna Ifeanyi Ede a yau dinnan Alhamis ya gurfana a gaban alkalin wata kotun Majistare a garin Abuja, babban birnin Najeriya bisa zargin sa da ake yi na cinnawa gidan budurwar sa wuta.
Da yake bayar da ba'asi, dan sanda mai gabatar da kara mai suna Idowu Lawal kamar yadda muka samu tun farko ya bayyanawa kotun cewa shi dai wanda yake tuhumar ya bankawa gidan budurwar sa mai suna Esther Yahaya dake zaune a garin Kubwa, Abuja wuta a ranar 5 ga watan Maris.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng