Wata 'Yar Kunar Bakin Wake Ta tayar da Bam a Masallacin Buni-Yadi
Wata 'yar kunar bakin wake ta kai hari kan massalata a wani masallacin yankin Fulatari na garin Buni-Yadi dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan hari ya afku ne da misalin karfe 5.30 na safiyar ranar Alhamis din ta gabata, inda aka yi sa'a wannan budurwa kadai ce ta riga mu gidan gaskiya tare da raunatar wasu mutane biyu.
Wannan shine hari na farko da ya afku a yanku tun daga ranar 16 ga watan Afrilu na shekarar 2016 da dakarun soji suka mamaye kauyen a shekarar 2015.
Wani mashaidin wannan lamari, Bulama, ya shaidawa manema labarai cewa budurwar tayi yunkurin afkawa masallancin sai dai wani Malam Yakubu yayi ta maza wajen tokare ta.
KARANTA KUMA: Wani 'Dan Majalisar Wakilai ya bayyana inda 'yan Matan Dapchi suke
Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Abdulmalik Sunmonu, ya tabbatar faruwar wannan lamari, inda ya ce Malam Yakubu yana karbar kyakkyawar kulawar likitoci a halin yanzu.
A yayin haka kuma, Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wani muhimmin dalili zai sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari amincewa da sauya kundin tsarin mulkin kasa kamar yadda majalisun tarayya da na jihohi suka bukata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng