Nigerian news All categories All tags
Yan matan Dapchi na nan cikin Yobe, cewar Dan majalisa, Goni Abubakar

Yan matan Dapchi na nan cikin Yobe, cewar Dan majalisa, Goni Abubakar

Wani dan majalisar, Mr Goni Abubakar ya ce yan matan Dapchi 110 da Boko Haram ta yi garkuwa da su a garin Dapchi a ranan 19 ga watan Fabrairu na nan cikin garin Yobe.

Dan majalisan ya yi ikirarin cewa an ajiyesu a Bulabuli, karamar hukumar Yunusari na jihar inda ya ce Boko Haram sun kwace shekaru 4 baya.

“Muna da masaniya cewa suna Bulabulin, karamar hukumar Yunusari. Hukumar tsaro na da ilimin cewa Boko Haram suna wurin shekaru 4 baya yanzu. Suna zaune a garin tamkar na su,” Bukar ya bayyanawa jaridar The Nation.

Yan matan Dapchi na nan cikin Yobe, cewar Dan majalisa, Goni Abubakar

Yan matan Dapchi na nan cikin Yobe, cewar Dan majalisa, Goni Abubakar

Dan majalisan mai wakiltan mazabar Bursari/Yunusari/Gaidam inda akayi garkuwa da yan matan. Yace shirye yake da nunawa soji inda aka ajiye yan matan.

KU KARANTA: Gobara ta lashe sama da shaguna 600 a kasuwar Bida

“Al’amarin ba wai aiki soji 10 ko soji 20, abinda muke bukata shine yi da gaske. Idan suka ga dama su bani kayan soji, zan sanya in nuna musu wajen.” Yace

Har yanzu dai hukumar soji basu mayar da martani

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel