Wani 'Dan Majalisar Wakilai ya bayyana inda 'yan Matan Dapchi suke
Hukumomin tsaro masu laluben 'Yan Matan Dapchi 110 da 'yan ta'addan Boko Haram suka yi garkuwa da su makonni biyu da suka gabata, sun samu 'yar alama a ranar Alhamis din da ta gabata dangane da inda 'yan matan suke a halin yanzu.
Wani 'Dan Majalisar Wakilai ya bayyana cewa, 'Yan Matan nan dai har yanzu suna cikin yankin jihar ta Yobe.
Goni Bukar, 'Dan Majalisar mai wakiltar Mazabun Bursari, Yunusari da kuma Gaidam, ya bayyanawa manema labarao na Jaridar The Nation cewa, 'Yan Matan suna garin Bulabulin dake karamar hukumar Yunusari ta jihar.
Dangane da fadi tashin da dakarun Soji suke na ceto 'yan Matan, 'Dan majalisar ya bayyana cewa babu shakka suna iyaka bakin kokarin su, hakazalika kuma ba su da laifi ko kadan akan wannan lamari da afku.
KARANTA KUMA: Ba bu laifin da Magu yayi kuma yana nan daram - Osinbajo
Rahotanni sun bayyana cewa, ana ci gaba da kwarara addu'o'i a fadin kasar nan domin samun nasarar ceto 'Yan Matan 110 cikon koshin lafiya.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi wasu sabbin jakadu uku na kasashen ketare a fadar sa ta Villa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng