Baƙonka Annabinka: Buhari ya samu baƙoncin wani ƙusa daga cikin ƙusoshin daular larabawa

Baƙonka Annabinka: Buhari ya samu baƙoncin wani ƙusa daga cikin ƙusoshin daular larabawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wani muhimmin bako, daya daga cikin kusoshi a daular larabawa, wanda ya tarbe shi a fadar gwamnatin Najeriya dake babban birnin Abuja.

Legit.ng ta ruwaito wannan bako ba wani bane illa mahaifin sarkin kasar Qatar, Sheikh Hmad Bin Khalifa Althani, wanda ya kawo ziyara don gina alakar kasuwanci da Najeriya.

KU KARANTA:Yaki da rashawa: Yadda wani tsohon minista ya lakume naira miliyan 840 cikin yan watanni

Baƙonka Annabinka: Buhari ya samu baƙoncin wani ƙusa daga cikin ƙusoshin daular larabawa

Buhari da Hamad

A jawabinsa, shugaba Buhari ya bayyana tsare tsaren da gwamnatinsa ta gudanar a shekaru biyu da suka gabata ya haifar da da mai ido, inda yayi sanadiyyar kwararowar masu zuba hannun jari Najeriya.

“Saninku ne cewar mun fita daga tabarbarewar tattalih arziki, kuma mun ninka adadin kudaden mu dake asusun ajiyan kudi na kasar waje, muna samun nasara a yaki da rashawa da muka sa a gaba, haka zalika muna gine ginen manyan ayyuka, bugu da kari kuma muna tabbatar da bin doka da oda.” Inji shi.

Baƙonka Annabinka: Buhari ya samu baƙoncin wani ƙusa daga cikin ƙusoshin daular larabawa

Buhari da Hamad

Inda yace wadannan matakan ne suka yi sanadiyyar da matasan Najeriya ke samun aikin yi fiye da a gwamnatocin baya. Bugu da kari Buhari ya sanar da su alakar kasuwanci da ya shiga da kasar Morocco, wanda a sanadin haka kamfanonin hada taki guda 13 sun farfado.

Da yake nasa jawabin, Sheikh Althani ya bayyana cewa martabar Najeriya ya karu a tsakanin kasashen duniya, don masu zuba hannun jari a kasuwannin Duniya sun tabbatar da Najeriya a matsayin kasar da yan kasuwa zasu iya zuba jari cikin kwanciyar hankali.

Baƙonka Annabinka: Buhari ya samu baƙoncin wani ƙusa daga cikin ƙusoshin daular larabawa

Buhari d Hamad

Althani yace hakan ya tabbata ne kadai sakamakon jajircewar da shugaba Buhari ya nuna game da yaki da rashawa da kuma tabbatar da bin doka da ka’ida.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel