A shirya nake inyi zaman Kurkuku – Inji wani Sanata da ya siya Makilin, Aswaki, Soso da Sabulu a Kotu

A shirya nake inyi zaman Kurkuku – Inji wani Sanata da ya siya Makilin, Aswaki, Soso da Sabulu a Kotu

Dan majalisar dattawa mai wakiltar al’ummar mazabar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya bayyana ma yan jaridu cewa a shirye yake ya yi zaman Kurkuku matukar Alkali ya yanke masa wannan hukunci.

The Cables ta ruwaito Melaye ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 1 ga watan Maris, a farfajiyar wat babbar Kotu dake zamanta a garin Abuja, jim kadan bayan kammala zaman sauraron karar da gwamnatin tarayya ta shigar da shi saboda kazafin da ya yi ma wasu wai sun shirya kashe shi.

KU KARANTA: Badakalar dala miiyan 44: Magu zai sha tambayoyi a majalisar wakilai na tsawon awanni 2

Dayake zantawa da manema labaru bayan kammala shari’ar, Melaye ya nuna musu kwalbar lemun Coke, makilin da kuma burushi, wato Aswaki, inda yace “A shirye nazo, da niyyar idan ma har Alkalin Kotun bai bada beli na ba, yace a tsare ni a Kurkuku.”

A shirya nake inyi zaman Kurkuku – Inji wani Sanata da ya siya Makilin, Aswaki, Soso da Sabulu a Kotu
Melaye

Gwamnati na tuhumar Melaye ne da yi ma shugaban ma’aikatan fadar shugaban gwamnatin jihar Kogi, Edward David kazafin wai ya aiko yan bindiga su kashe shi, haka zalika ana tuhumarsa da bada bayanan karya ga Mohammed Abubakar, yaron tsohon gwamnan jihar Abubakar Audu, da nufi bata ma Edward suna.

Sai dai bayan sauraron lauyoyin masu kara da wanda ake kara, sai Alkalin Kotun, Olasumbo Goodluck ya bada belinsa akan kudi naira 100,000, daga nan kuma y adage shari’ar zuwa ranakun 16 da 17 na watan Mayu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng