Wanda ya ki ji, baya ki gani ba: Wani Saurayi dake neman matan aure da tsakar dare ya shiga hannu
Wani matashi mai shekaru 25, Bilyaminu Sunusi ya gurfana gaban wata Kotun majistri, inda ake tuhumarsa da laifin neman wata matar aure a waya da tsakar dare, inji rahoton Premium Times.
Dansanda mai kara, Umar Rabiu ya gurfanar da Bilya ne a ranar Alhamis 1 ga watan Maris, bayan mijin matar Abdulkadir Ibrahim ya kai musu kara a caji ofis, inda yace Bilya ya aikata wannan laifi ne a cikin watan Janairun bana.
KU KARANTA: Labari cikin Hotuna: Gwamnonin Arewa yayin da suke gudanar da taro kan tashe tashen hankula da ya addabi yankin
Dansandan ya bayyana ma Kotu cewar mijin matar ya fada musu wata lamba 0817675917 na yawan kiran matarsa da tsakar dare yana tambayarta ‘Har kin yi barci ne?”, daga nan ne fa Yansanda suka dukufa wajen bincike, har suka gano ashe lambar Bilya ne.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dansandan yan cewa laifin da ake tuhumar Bilya da shi ya saba ma sashi na 389 na kundin hukunta manyan laifuka, sai dai Bilya ya musanta wannan zargi da ake yi masa.
Bayan sauraron dukkanin bangarorin, sai Alkalin Kotun Abubakar Adamu ya bada belinsa akan kudi N100,000, tare da mutum guda da zai tsaya masa akan kudi N100,000 shi ma, daga nan kuma ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Maris.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng