Labari cikin Hotuna: Gwamnonin Arewa yayin da suke gudanar da taro kan tashe tashen hankula da ya addabi yankin

Labari cikin Hotuna: Gwamnonin Arewa yayin da suke gudanar da taro kan tashe tashen hankula da ya addabi yankin

Sakamakon yawan tashe tashen hankula da ake yawan samu a yankin Arewacin kasar nan, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama da kuma tarin dukiyoyi, gwamnonin Arewa sun shirya yi ma tufkar hanci.

A ranar Alhamis 1 ga watan Maris ne dai gwamnonin suka dunguma zuwa jihar Kaduna, da nufin tattaunawa batutuwan da suka shafi rikice rikice da fadace fadace dake faruwa a tsakanin al’ummar yankin.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Yadda wani tsohon minista ya lakume naira miliyan 840 cikin yan watanni

Labari cikin Hotuna: Gwamnonin Arewa yayin da suke gudanar da taro kan tashe tashen hankula da ya addabi yankin
Labari cikin Hotuna

Wannan taro dai ya gudana ne a dakin taro na fadar gwamnatin jihar Kaduna, dake gidan Sir Kashim Ibrahim, kuma ya samu halartar shugaban gwamnonin Borno Kashim Shettima, da kuma gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, Kogi Yahaya Bello, Kebbi Atiku Bagudu, Neja Abubakar Sani.

Sauran sun hada da gwamnan jihar Katsina, AMinu Bello Masari da kuma gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abubakar, sai kuma mataimakan gwamnoni da sakatarorin gwamnati da suka wakilci sauran gwamnonin jihohin yanikin.

Labari cikin Hotuna: Gwamnonin Arewa yayin da suke gudanar da taro kan tashe tashen hankula da ya addabi yankin
Labari cikin Hotuna

Legit.ng ta ruwaito ko a yan kwanakin nan sai da aka samu rikicin addini a wasu sassan jihar Kaduna da suka kunshi, garin Maran rido, kauyen Kalla da kuma kasuwar magani, and ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

Labari cikin Hotuna: Gwamnonin Arewa yayin da suke gudanar da taro kan tashe tashen hankula da ya addabi yankin
Labari cikin Hotuna

Hakazalika ga kuma batun rikicim Boko Haram da yaki ci, ya ki cinyewa, duk da nasarar karya lagon kungiyar yan ta’addan da rundunar Sojojin Najeriya ta yi, amma ko a satin da ta gabata sai da suka saci ya mata 110.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng