Gwamnatin Buhari zata sake kashe naira biliyan 16.6 don gudanar da ayyukan titiuna a kudancin kasar nan
Gwamnatin tarayya ta kammala shirye shiryen sake zuba tsabar kudi har naira biliyan 16.6 daga cikin kudin SUKUK don gudanar da ayyukan gyagyaren hanyoyi tare da gina sabbi a yankin kudu maso gabashin kasar nan.
Vanguard ta ruwaito tun a watan Oktoban shekarar 2017 ne dai gwamnatin shugaba Buhari ta sakr kudi naira biliyan 100 da aka samo su daga bankin Musulunci, wanda za ta kashe su akan manyan hanyoyi masu muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya guda 25 a dukkanin sassan kasar.
KU KARANTA: Badakalar dala miiyan 44: Magu zai sha tambayoyi a majalisar wakilai na tsawon awanni 2
Daraktan kula da manyan hanyoyin kudu maso gabashin kasar nan, na ma’aikatan ayyuka, Adetokunbo Sogbesan ne ya bayyana haka a ranar Laraba a yayin ziyarar aiki da ya kai ma wasu manyan ayyuka da gwamnatin ke yi a yankin.
Ya lissafa hanyoyin da zasu mayar da hankali a kai da suka hada da Enugu-Onitsha, Enugu-Lokpanta, Lokpanta-Abia, da kuma Abia-Aba- Fatakwal, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
Da yake duba aikin sashin titin Mil 9 zuw Enugu, Daraktan ya nuna farin cikinsa da yanayin aikin da dan kwangilar ya yi, inda yace aikin na kilomita 58 ya daga Amansea zuwa Enugu ya cika dukkanin sharuddan gina titi, inda ya kara da cewa Titin ka iya kwashe shekaru 20 ba tare da ya samu matsala ba.
Sai dai Daraktan ya koka da yawan ababen hawa dake bin kan titin, don haka yayi fatan su samu isassun kudade domin aikin titin ya kammala a cikin lokaci, ana sa ran kammala akin a watan Disambar shekarar 2019, inda aka faro shi a watan Janairun 2017.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban kamfanin dake kwangilar titin, Mista Italy ya yaba ma matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na ganin kamfanunuwa na amfani da yan Najeriya a matsayin ma’ikatansu, inda yace suna aiki da yan Najeriya 650 akan titin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng