Zanyi amfani ta kowacce hanya don mayar da Saudiyya kasar zamani
- Yariman kasar Saudiyya ya bayyana cewa zai yi amfani da duk wata hanya da ta dace domin magance matsalar cin hanci da rashawa a kasar
- Sannan ya ce zai yi iya bakin kokarin sa wurin ganin ya maida kasar ta zama ta zamani
- Ya ce hakan shine zai kawo bunkasar tattalin arziki a kasar
Yariman kasar Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salman ya bayyana cewa, zai yi amfani da hanyar da ta dace wajen magance cin hanci da rashawa dake addabar kasar, wanda hakan hanya ce ta mayar da kasar ta zamani.
DUBA WANNAN: To fa wata sabuwa: Wani Bayahude ya kai karar abin bautar sa kotu
Yariman wanda ya tattauna da manema labarai ya ce, cin hanci da rashawa ya kama kasar ta Saudiyya kamar yanda ciwon daji ke kama jikin dan adam, kuma zai yi amfani da hanyar da ta dace wurin magance cutar.
Yariman mai shekaru 32 ya ce, hanyar da za abi domin mayar da saudiyya kasar zamani da raya al'adu abu ne kamar maganin cutar daji mai amfani da shokin din lantarki.
Yariman yayi watsi da maganar da mutane ke yi na cewa, ya watsar da ayyukan da Sarki Abdulaziz bin Suud, wanda shine mutumin daya kafa masarautar Saudiyyar, inda shi kuma ya maida martani da cewa su suna kokarin kawo abubuwan zamani ne kasar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng