Nigerian news All categories All tags
To fa wata sabuwa: Wani Bayahude ya kai karar abin bautar sa kotu

To fa wata sabuwa: Wani Bayahude ya kai karar abin bautar sa kotu

- Ya kai karar Allan sa kotu a kasar Isra'ila

- Ya kai shi gaban kotun bisa zargin yana yi mashi shisshigi a harkar rayuwar sa

- Ya bukaci kotu ta shiga tsakanin su, sannan ta bi masa hakkin sa

To fa wata sabuwa: Wani Bayahude ya kai karar abin bautar sa kotu

To fa wata sabuwa: Wani Bayahude ya kai karar abin bautar sa kotu

Zuwa yanzu dai babban alkalin kotun yankin Haifan na kasar Isra'ila ya kasa share wa wani Bayahude kwallar sa, wanda ya kai karar abin bautar sa kotu, a watannin da suka gabata.

Mai karar ya nemi kotu da ta tsawatar wa ubangijin na shi da ya daina yi masa shisshigi a cikin al'amuran sa na rayuwa.

DUBA WANNAN: Saura kadan a sanya hannu akan kudurin rage shekarun tsayawa takara - Not too young to run

A zaman da aka yi na farko na shari'ar, mai karar wanda ba a bayyana sunan sa ba, ya ce abin bautar nasa yana zaluntar shi babu gaira babu dalili, abinda yasa yazo gaban kotu kenan domin abi masa hakkin sa.

A lokacin, alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa wata na gaba, saboda ya ce wanda ake tuhuma din bai halarci shari'ar ba.

Hakan ne ya jawo mai karar ya dinga korafi yana cewa, ana yi masa rufa-rufa ne, saboda ga dukkan alamu babu mai niyyar share hawayensa. Ya ce, kusan shekaru uku kenan da yake ta faman kai kawo a helkwatar hukumar 'yan sanda, domin a hana abin bautar nashi takurawa rayuwarsa, amma kawo yanzu babu wani kokari da suka yi na biya masa bukatar sa.

An shafe watanni da dama ba tare da an sake zaman shari'ar ba, saboda lamarin yayi matukar daurewa alkalin da kuma al'ummar duniya baki daya kai.

Bayan an dauki dan lokaci, alkalin yankin Haifa, Ahsan Canaan ya sake dawo da batun shari'ar wanda ya hana shi runtsawa, inda a zaman karshe da aka yi a baya bayan nan, ya ce shari'ar tafi karfin sa. Ya kara da cewa, idan mai karar na son a share masa hawaye sai dai ya kai karar ta shi wani wurin daban.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel